logo

HAUSA

Sin ta gudanar da bukukuwa don tunatar da al’umma a kan harin Japanawa na ran 18 ga watan Satumban 1931

2022-09-18 17:05:00 CMG Hausa

An kunna jiniya da karfe 9:18 na safiyar Lahadin nan, a gidan adana kayan tarihi na harin Japanawa na ran 18 ga watan Satumban 1931 da ke birnin Shenyang, fadar mulkin lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin, a yayin da kuma aka gudanar da sauran ayyuka a sassa daban daban na kasar, domin tunatar da al’umma a kan harin da sojojin kasar Japan suka kaddamar a ranar 18 ga watan Satumbar 1931.

A rana irin ta yau a shekarar 1931, sojojin kasar Japan suka tarwatsa wani sashe na layin dogo dake birnin Shenyang, tare da zargin sojojin kasar Sin da aikata hakan, daga bisani kuma suka yi amfani da wannan dalili, suka kai hari kan dakarun bataliyar Sin dake Beidaying, suka kuma kaddamar da harin bam kan birnin Shenyang da daren wannan rana, kafin kuma su kaddamar da cikakkiyar mamaya a yankin arewa maso gabashin kasar ta Sin.

Ana gudanar da bikin wannan rana ne a matsayin tunatarwa, dangane da mawuyacin hali da Sinawa suka tsinci kan su ciki a lokutan baya. Tarihi na sha nuna yadda mamaya, da yake yake ke karewa ba tare da cimma wata nasara ba, kuma ko da an yi kokarin boye gaskiya, daga karshe adalci ne ke yin nasara.  (Saminu Alhassan)