logo

HAUSA

An soki wakilin Amurka game da batun sauyin yanayi a Afrika

2022-09-18 16:57:04 CMG Hausa

Babban daraktan cibiyar Climate Justice Alliance ko PACJA, mai rajin kare muhalli a nahiyar Afirka Mithika Mwenda, ya soki lamirin wakilin Amurka mai lura da batun sauyin yanayi John Kerry, bisa yadda ya nuna halin ko in kula, game da mummunan tasirin da sauyin yanayi ke yi ga kasashen Afirka.

Mwenda, ya zargi Amurka da gaza cika alkawuran da ta furta, game da tallafawa nahiyar Afirka da albarkatun rage tasirin iskar Carbon mai dumama yanayi, domin kare yanayi a nan gaba.

Yayin taron ministocin kasashen Afirka game da kare muhalli ko AMCEN, wanda ya gudana tsakanin ranekun 13 zuwa 16 ga watan nan, a birnin Dakar na kasar Senegal, an jiyo Mr. Kerry na furta wasu kalamai, na nuna halin ko in kula game da radadin da kasashen Afirka ke sha daga tasirin sauyin yanayi, yana mai cewa, kasashen yamma ba su da wani alhaki game da wannan matsala dake addabar nahiyar Afirka, ko ma duk wasu kasashe masu tasowa.

Game da hakan, Mr. Mwenda, ya bayyana rashin jin dadin sa ga kalaman na Mr. Kerry, yana mai cewa, hakan ya shaida yadda Amurka, da sauran kasashen yamma ke yin watsi da alkawuran da suka dauka ga nahiyar Afirka. Mwenda ya ce mafi yawan manyan kasashen yammacin duniya, ba su cika alkawuran su ga Afirka ba, wanda hakan ke kara ingiza matsaloli masu nasaba da sauyin yanayi, kamar talauci da tashe tashen hankula da barkewar cututtuka.   (Saminu Alhassan)