logo

HAUSA

‘Yan sama jannatin Shenzhou-14 sun kammala ayyuka a wajen dakin gwaji na Wentian

2022-09-18 16:43:53 CMG Hausa

‘Yan sama jannatin kasar Sin 3 da suka tashi da kumbon Shenzhou-14, sun kammala ayyuka a wajen dakin gwaji na Wentian cikin nasara, kamar dai yadda hukumar lura da ayyukan sama jannati ta kasar CMSA ta bayyana a jiya Asabar.

CMSA ta ce ya zuwa karfe 1:35 na jiya bisa agogon birnin Beijing, dan sama jannati Cai Xuzhe ya bude kofar dakin gwaji na Wentian, kana da misalin karfe 3:33, shi da abokin aikin sa Chen Dong, dukkansu sun fita wajen dakin gwajin. Ma’aikatan su biyu, sun koma cikin dakin gwajin da misalin karfe 6 saura mintuna 13, bayan kammala ayyuka na tsawon sa’o’i 5, da taimakon ‘yar sama jannati Liu Yang, dake tallafa musu a cikin dakin gwajin.

Ayyukan da ‘yan sama jannatin suka gudanar a wajen dakin gwajin, sun hada da kafa na’urorin taimakawa tattaki a wajen kumbon, da sauran wasu kayan laturori da ake bukata domin gudanar da ayyuka, kana sun tantance ingancin tsarin ayyukan ceto a wajen kumbon.

Bugu da kari, jami’an sun sake nazartar tsare tsaren ayyukan sama jannati, da na hannun butumbutumi da aka tanada, da kuma ingancin na’urar killace iska dake cikin dakin gwajin na Wentian, da sauran na’urorin dake taimakawa ayyukan tattakin a wajen dakin gwajin. (Saminu Alhassan)