logo

HAUSA

USA Today: Amurkawa bakaken fata suna so a biya zuriyar bayin da aka bautar diyya

2022-09-17 16:28:02 CMG Hausa

A wannan mako kafofin watsa labaran Amurka, sun ruwaito wani rahoton binciken da cibiyar bincike ta Pew ta gudanar dake nuna cvewa, kimanin kashi 77 cikin 100 na Amurkawa bakaken fata, sun bayyana cewa, ya kamata, zuriyar mutanen da aka bautar a tarihin kasar, a biya su diyya.

Sai dai kuma, a cewar rahoton yawancin wadanda aka zanta da su, ba sa tunanin cewa, za a biya bakaken fatan diyyar, ko da yake, kungiyoyin kabilu da wasu Amurkawa sun dade suna fatan ganin hakan ya tabbata.

Cibiyar bincike ta Pew ta bayyana a cikin rahoton nata cewa, gaba daya, baligai bakaken fata, ba su da tabbacin game da yiwuwar biyan diyyar, amma da dama daga cikinsu, sun bayyana cewa, ya kamata gwamnatin tarayyar Amurka, ta dauki nauyin biyan diyyar baki daya ko kaso mafi yawa daga ciki.

Kimanin kashi 45 cikin 100 na Amurkawa bakaken fata, sun ce da wuya a samu daidaito. Bugu da kari, kusan mutum 9 cikin 10 na baligai babaken fata, suna son ganin an yi gyaran fuska ga bangarorin kotuna da sauran sassan tsarin shari'ar manyan laifuffuka.

A cewar wani rahoto da jaridar Amsterdam News ta fitar, jaridar dake ba da rahoto kan babaken fata da ke birnin New York, akwai Amurkawa bakaken fata da dama da ake tsare da su a gidajen yari a fadin Amurka.

Da take bayani kan wani rahoto game da wadanda ake tsare da su a gidan yari, mai suna “The Sentencing Project”, jaridar ta ce Amurkawa bakaken fata, suna wakiltar kashi 14 cikin 100 na jimlar Amurkawa, kashi 33 cikin 100 na jimlar yawan fursunoni, da kashi 46 na yawan fursunonin da suka riga suka shafe shekaru 10 a tsare.(Ibrahim)