logo

HAUSA

Wang Yi ya tattauna ta wayar tarho da mai baiwa shugaban Faransa shawara kan harkokin diflomasiyya

2022-09-17 21:12:59 CMG Hausa

Yau ne, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho da mai baiwa shugaban Faransa Emmanuel Macron shawara kan harkokin diflomasiyya Emmanuel Bonne.

Wang Yi ya ce, ci gaba da wanzuwar dangantakar kasashen biyu yadda ya kamata, ya dace da moriyar kasashen biyu, kuma yana ba da gudummawa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.(Ibrahim)