logo

HAUSA

Wakilin musamman na Xi zai halarci jana'izar sarauniya Elizabeth ta biyu

2022-09-17 16:13:10 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta sanar a yau Asabar cewa, bisa gayyatar da gwamnatin kasar Birtaniya ta yi masa, wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mataimakin shugaban kasar Wang Qishan, zai halarci jana'izar sarauniya Elizabeth ta biyu da za a yi a birnin Landan a ranar Litinin 19 ga watan Satumba.(Ibrahim)