logo

HAUSA

Wakilin Sin ya bukaci kwamitin sulhu da ya soke takunkuman da ya kakabawa Sudan ta kudu

2022-09-17 16:10:22 CMG Hausa

Jiya Jumma’a mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Dai Bing, ya gabatar da wani jawabi yayin taron tattaunawa kan batun kasar Sudan ta kudu da kwamitin sulhun majalisar ya kira, inda ya bukaci kwamitin sulhun, da ya gaggauta soke takunkuman hana jigilar makamai da ya kakabawa kasar Sudan ta kudu.

Dai Bing ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, yanayin siyasa na Sudan ta kudu ya shiga wani sabon mataki mai muhimmanci, bangarori daban daban da suka sa hannu kan yarjejeniyar sake farfado da Sudan ta kudu, sun cimma ra’ayi daya da jadawalin tsawaita wa’adin mika mulki a kasar a watan jiya, shawarar da suka yanke ta dace da yanayin da ake ciki yanzu, kana za ta samar da zaman lafiya a kasar. Don haka, ya dace sauran kasashe duniya su fahimci matsalar da Sudan ta kudu take fuskantar, su fahimci shawarar da aka yanke, kada su yi amfani da shirya zabe a matsayin wata dabara ta daidaita daukacin hargitsi, kuma bai kamata a yi watsi da kokarin gudanar da tattaunawar shimfida zaman lafiya da bangarori daban daban na Sudan ta kudu suke yi ba.

Dai Bing ya kara da cewa, yanzu haka an yi nasarar yaye tare da jibge kashin farko na rundunar sojojin kasar Sudan ta kudu lami lafiya, wannan babban ci gaba ne da aka samu yayin tabbatar da yarjejeniyar sake farfado da kasar, matakin da ya alamta cewa, aikin shimfida zaman lafiya ta Sudan ta kudu, ya samu sabon ci gaba. Amma takunkuman da kwamitin sulhun MDD ya kakabawa Sudan ta kudu, yana da illa ga rundunar sojojin Sudan ta kudu na samu makaman da take bukata domin gudanar da aikinta, don haka kasar Sin ta sake yin kira ga kwamitin sulhun majalisar, da ya mai da hankali kan bukatun Sudan ta kudu, ya gaggauta soke takukumnan da ya kakabawa kasar, don taimakawa Sudan ta kudu wajen kara karfinta na tabbatar da tsaro a kasar. (Jamila)