logo

HAUSA

Wang Yi zai halarci babban taron MDD karo na 77 da sauran manyan ayyukan da abin ya shafa

2022-09-17 19:46:13 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta sanar a yau Asabar cewa, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, zai halarci babban taron MDD karo na 77 da zai gudana daga ranar 18 zuwa 25 ga watan Satumban da muke ciki.

A tsawon wannan lokaci, Wang Yi zai jagoranci taron ministocin "Rukunin aminan shirin raya kasa na duniya", zai kuma halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen BRICS dake babban zauren MDD da sauran ayyuka, zai kuma gana da babban sakataren MDD, da shugaban babban taron MDD karo na 77, gami da shugabannin tawagogin wasu kasashe. (Ibrahim)