logo

HAUSA

Tattalin arzikin Sin yana ta farfadowa a watan Agusta

2022-09-16 19:35:02 CMG HAUSA

 

Bisa kididdigar da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a yau Juma’a, tattalin arzikin al’ummun kasar Sin ya farfado ya zuwa watan Agusta, kuma bukatun samar da hajoji yana ta karuwa sannu a hankali, kana guraben aikin yi da farashin kayayyaki dukkansu ba su yi tangarda ba, kaza lika yawancin ma’aunan da suke bayyana yadda ake samun ci gaba a watan Agusta sun zarta na watan Yuli.

Hukumar ta kuma ce, duk da haka, ya kamata a lura da cewa, har yanzu yanayin kasa da kasa yana da sarkakiya da kuma tsanani, kuma ginshikin farfadowar tattalin arzikin cikin gidan kasar Sin har yanzu ba shi da inganci kamar yadda ake fata. (Safiyah Ma)