logo

HAUSA

Taron majalisar shugabannin kasashen SCO karo na 22 ya cimma nasarori da dama

2022-09-16 19:55:08 CMG Hausa

Yau ne, aka shirya taron majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai karo na 22 a cibiyar taron kasa da kasa ta Samarkand.

Shugabannin kasashen kungiyar, sun sanya hannu tare da fitar da sanarwar ganawar majalisar shugabannin kasashen kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da ya gudana a Samarkand.

Taron ya fitar da bayanai da takardu masu tarin yawa, game da tabbatar da samar da abinci da makamashi na kasa da kasa, da magance matsalar sauyin yanayi, da tabbatar da tsaro, da kwanciyar hankali, da daidaita da ma fadada tsarin samar da kayayyaki, inda aka sanya hannu kan wata yarjejeniya game da wajibcin kasar Iran na shiga kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, da fara shirye-shiryen karbar kasar Belarus a matsayin mamba, da amincewa da kasashen Masar, da Saudiya, da Qatar, da Bahrain, da Maldives, da hadaddaiyar daular Larabawa, da Kuwait, da Myanmar a matsayin sabbin abokan tattaunawa.(Ibrahim)