logo

HAUSA

Wakilin kasar Sin: Shawarar “ziri daya da hanya daya” hanya ce ta hadin kai da samun nasara

2022-09-15 14:42:50 CMG Hausa

Tawagar kasar Sin dake MDD ta fitar da wani rahoto mai lakabi “yin aiki tare don neman samun makoma mai kyau——rahoto kan yadda shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ take goyon bayan muradun ci gaba masu dorewa nan da shekarar 2030 na MDD”.

Tawagar ta Sin da hukuma mai kula da harkokin tattalin arziki da zaman al’umma ta MDD su ne suka fitar da rahoton jiya Laraba cikin hadin gwiwa.

A cikin jawabin da wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya bayar, ya bayyana cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya” ita ce dabara da basirar Sin wajen aiwatar da muradun MDD na 2030, wadda ta dace sosai a fannonin ra’ayoyi da mukasudi da matakai, kuma ta nuna goyon baya da kuma kuzari wajen gudanar da mukasudin ci gaba mai dorewa. Ya kara da cewa, bangaren Sin yana fatan zurfafa hadin gwiwa a fannoni iri iri da inganta ci gaban “ziri daya da hanya daya” tare da dukkan abokai  dake cikin hadin gwiwar, da kuma ba da gudummawa wajen inganta muradun MDD na 2030 cikin sauri da kuma cimma hadin gwiwa tare da kasashen duniya.

Jakadun kasashen duniya da wakilan hukumomin MDD dake halartar taron sun taya murnar fitowar rahoton tare, kana sun yabi shawarar “ziri daya da hanya daya” sosai don ta taimakawa kasashen duniya wajen yakar talauci da bunkasa tattalin arziki da mu’ammala da juna, sun kuma yi imanin shawarar “ziri daya da hanya daya” za ta taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da muradun ci gaba masu dorewa na MDD na 2030. (Safiyah Ma)