logo

HAUSA

Kasar Sin ce take kan gaba a duniya a yawan na'urorin makamashin nukiliya da ake ginawa

2022-09-15 20:45:28 CMG Hausa

Wani shudin kundi da kungiyar makamashin nukiliya ta kasar Sin (CNEA) ta fitar jiya Laraba, ya nuna cewa, kasar Sin na ci gaba da jagorantar duniya, a yawan tashoshin makamashin nukiliya da ake ginawa.

Ya zuwa karshen watan Agusta, kasar Sin tana da rukunin makamashin nukiliya na kasuwanci 53 masu jimillar karfin gigawatts 55.59 da aka kafa, yayin da ake kan gina wasu sassa guda 23 masu karfin gigawatt 24.19 baki daya. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)