Matsalar Bindiga Tana Addabar Amurka Matuka
2022-09-15 10:35:38 CMG Hausa
Yau watanni 3 da suka wuce, wani dan bindiga ya kashe kananan yara 19 da malamai 2 a makarantar firamare ta Robb a kasar Amurka. A lokacin, shugaba Joe Biden na kasar ya lashi takobin daukar hakikanin matakai, tare da sa hannu kan shirin dokar kayyade sayen bindiga a watan Yuni, wanda a cewarsa, shirin doka ne mafi muhimmanci cikin shekaru 30 da suka wuce kan harkokin bindiga. Amma fararen hula da ba su ji ba su gani ba suna mutuwa sakamakon harbe-harben bindiga.
A karshen makon jiya, an yi harbe-harbe a wasu jihohin Amurka. Me ya sa Amurka, wadda ke matsayin kasa mafi arziki a duniya, ba ta sa aya ga laifuffuka masu nasaba da bindiga ba? Masharhanta sun yi nuni da cewa, dalilan da suka sa hakan su ne: tanade-tanaden dake cikin gyararren shirin doka na 2 na kundin tsarin mulkin kasar dangane da mallakar bindiga, da kuma sabanin dake tsakanin jam’iyyun siyasa 2 na Amurka kan sa ido kan harkokin bindiga.
Har ila yau, matsalar bindiga tana yin kamari sakamakon yawan riba. Girman kasuwar kera bindiga da cinikin bindiga ya kai dalar Amurka biliyan 70.5 a kasar a shekarar 2021. Kungiyar kula da harkokin bindiga ta Amurka NRA wadda ke matsayin rukunin tattalin arziki mafi tasiri a kasar, tana ba da taimakon kudi ta fuskar siyasa a kowace shekara, tare da zuba makudan kudade kan yayata muhimmancin mallakar bindiga bisa doka, a kokarin kawo tsaiko ga yadda gwamnatin take daukar matakai masu nasaba da bindiga.
Kamar yadda jaridar The New York Times ta bayyana, kusan kowa da kowa na rayuwa cikin tsoro a kasar Amurka sakamakon karuwar harbe-harben bindiga a kasar. Me ya sa haka? Domin masu kudi suna jin dadin ganin karuwar dukiyoyinsu sakamakon kera bindiga da cinikinsa, kana ’yan siyasan Amurka suna ta samun taimakon kudi ta fuskar siyasa ba tare da tsayawa ba. Har zuwa yanzu ba a san yaushe Amurka za ta fitar da kanta daga yanayin tsoro sakamakon matsalar bindiga ba. (Tasallah Yuan)