logo

HAUSA

Wakilin Sin a MDD ya yi kira da a sassauta takunkuman da aka kakabawa Sudan

2022-09-14 10:40:44 CMG Hausa

 

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing ya yi kira da a sassauta takunkuman da aka kakabawa kasar Sudan game da batun yankin Darfur, ta yadda sannu a hankali za a kai ga janye su baki daya. Dai Bing ya yi wannan kira ne a jiya Talata. Yana mai cewa, takunkuman na haifarwa gwamnatin Sudan babban kalubale, a kokarinta na wanzar da daidaito, da kare fararen hula dake yankin Darfur.

Jami’in ya ce, Sin na matukar takaicin gazawar kwamitin tsaron MDD, wajen daidaita takunkuman har bayan ranar 31 ga watan Agusta, sabanin kudurin da aka cimma don gane da hakan.

Daga nan sai ya yi kira ga sassa masu ruwa da tsaki, da su himmatu wajen sauke nauyin alkawura da suka dauka, tare da komawa gudanar da shawarwari ba tare da bata lokaci ba, kana a kara azama wajen cimma matsaya. (Saminu Alhassan)