logo

HAUSA

Xi ya yi bayani game da matsayi da fifikon dangantakar dake tsakanin Sin da Kazakhstan

2022-09-14 20:56:32 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Kazakhstan Tokayev a birnin Nur-Sultan, fadar mulkin kasar ta Kazakhstan.

Xi Jinping ya bayyana cewa, ya yi matukar farin cikin sake ganawa da takwaransa na Kazakhstan. Yana mai cewa, wannan ita ce ziyararsa ta farko zuwa kasashen waje, tun bayan barkewar annobar COVID-19, kuma ya zabi zuwa kasar Kazakhstan, wadda ta nuna babban matsayi na daban kan alakar dake tsakanin kasashen biyu. Kasar Sin za ta ci gaba da zama aminiyar kawa kuma abokiyar huldar Kazakhstan. (Ibrahim)