logo

HAUSA

Najeriya: Ma’aikatan sufurin jiragen sama sun yi zanga zanga bisa wani kudurin doka

2022-09-13 14:00:52 CMG Hausa

Ma’aikatan sashen sufurin jiragen sama na tarayyar Najeriya, sun gudanar da zanga zangar lumana, ta nuna rashin amincewa da wani tanadin doka da ya haramta musu gudanar da zanga zanga.

A jiya Litinin ne dai daukacin ma’aikatan, karkashin kungiyar NUATE, suka yi yajin aikin yini daya, suna masu baiwa gwamnatin tarayyar kasar wa’adin makwanni 2, da ta yi watsi da tanadin dokar kafin su tsunduma dogon yajin aiki, tare da durkusar da ayyukan sufurin jiragen sama gaba daya.

A cewar shugaban kungiyar ta NUATE Ben Nnabue, ’ya’yan kungiyar sun gudanar da yajin aikin gargadi a dukkanin biranen kasar, ciki har da birnin tarayyar kasar Abuja, da jihar Lagos cibiyar kasuwancin kasar.

Nnabue ya ce, an cusa wani kuduri mai hadari cikin sabuwar dokar ayyukan sashen na sufurin jiragen sama, wadda ake sa ran shugaban kasar Muhammadu Buhari zai sanyawa hannu, don haka mambobin NUATE, a shirye suke da su shiga yajin aikin sai baba ta gani, wanda zai dakatar da dukkanin ayyuka a filayen jiragen saman kasar, idan har ba a janye wancan tanadin doka ba.  (Saminu Alhassan)