logo

HAUSA

IAEA: Za A Tattauna Batun Hadin Gwiwa Tsakanin Amurka Da Birtaniya Da Australiya

2022-09-13 11:11:41 CMG Hausa

 

An bude taron kwamitin hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA a birnin Vienna, hedkwatar kasar Austria jiya Litinin 12 ga wata, inda a karo na 4 a jere, aka cimma daidaito kan ayyana abun da ke shafar hadin gwiwa tsakanin kasashen Amurka, da Birtaniya da Australiya, a matsayin batun da za a tattauna.

Dangane da lamarin, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD a Vienna Wang Qun, ya bayyana wa manema labaru cewa, sakamakon shawarar da kasar Sin ta gabatar, ya sa kwamitin hukumar IAEA ta cimma daidaito a karo na 4 a jere, kan gudanar da tattaunawa game da illolin da za su shafi yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya wato NPT, sakamakon yin musayar kayayyaki masu nasaba da nukiliya, a tsakanin Amurka, Birtaniya, da Australiya, dangane da jiragen ruwan karkashin ruwa masu amfani da makamashin nukiliya, da yadda za a ba da tabbaci da sa ido a kai, lamarin da ya bankado wani yunkuri na wasu kasashe, na tilastawa kwamitin ya bi umurninsu. Don haka dai kawancen da Amurka ta kulla bai samu amincewar IAEA ba.

Wang Qun ya jaddada cewa, batun yin musayar kayayyaki masu nasaba da nukiliya a tsakanin Amurka, da Birtaniya, da Australiya, dangane da jiragen ruwan karkashin ruwa masu amfani da makamashin nukiliya, batu ne da ke shafar yaduwar makaman nukiliya. Don haka ya zama tilas kasashen 3, su dakatar da abun da suke yi, wanda zai kawo illa ga baki dayan duniya.

Jakadan na Sin ya yi fatan cewa, kasashe mambobin IAEA, za su mai da hankali kan batun, da kuma gaskiyar batun ta hanyar tattaunawa, a kokarin lalubo bakin zaren daidaitawa, da daukar hakikanin matakan kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya. (Tasallah Yuan)