logo

HAUSA

An gano ayyukan kutsen yanar gizo da NSA ta Amurka ta yi wa wata jami’ar kasar Sin

2022-09-13 15:57:44 CMG Hausa

A yau Talata ne mahukuntan kasar Sin suka fitar da wani rahoto, wanda ya bayyana yadda hukumar tsaron sirri ta Amurka ko NSA, ta yi amfani da wata kafa mai lakabin TAO, wajen yin kutse a na’urori masu kwakwalwa na jami’ar koyar da ilimin fasahohi, ko Northwestern Polytechnical University.

A cewar sashen kandagarkin kutsen na’ura mai kwakwalwa ta kasar ko CVERC a takaice, a baya bayan nan, kafar TAO ta yi amfani da matakan kutse 41, ciki har da wata manhaja mai lakabin "Suctionchar", wadda ake amfani da ita wajen satar tarin bayanai masu muhimmanci.

Wani kwararre a sashen na CVERC, ya ce bayan tantance abubuwan da suka faru, an gano cewa, hukumar NSA ta Amurka, na amfani da manhajar "Suctionchar", tare da wasu karin manhajojin wajen yin kutse da satar bayanai masu yawa a karin wasu na’urori masu kwakwalwa, ta hanyar gano lambobin sirrin da aka sata tun da farko, daga kwamfutoci da sassan yanar gizo daban daban. (Mai Fassarawa: Saminu Alhassan)