logo

HAUSA

Sin ta damu da rahoton da darektan IAEA ya fitar

2022-09-13 19:17:06 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Mao Ning, ta bayyana cewa, kasar Sin ta lura da rahoton da babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) ya fitar, game da batutuwan dake shafar hadin gwiwar jirgin ruwan karkashin teku mai amfani da makamashin nukiliya tsakanin kasashen Amurka da Birtaniya da Australia. Kasar Sin ta yi imanin cewa, wannan mataki ne dake bisa turba, amma ta damu matuka game da ainihin shi kansa rahoton.

A yayin taron manema labaru da aka kira Talatar nan, Mao Ning ta kuma bayyana cewa, ta'addanci makiyin daukacin bil-adama ne, kuma kasar Sin za ta ci gaba da taka rawar da ta dace, wajen yin hadin gwiwa da kasa da kasa a fannin yaki da ta'addanci, tare da ba da sabbin gudummawa ga ayyukan yaki da ta'addanci na duniya. (Ibrahim)