logo

HAUSA

An rufe babban taron MDD karo na 76

2022-09-13 10:57:23 CMG Hausa

An rufe babban taron MDD karo na 76 a jiya Litinin, inda shugaban taron na wannan karo Abdulla Shahid ya gabatar da jawabi, bayan da aka rantsar da Csaba Korosi daga kasar Hungary, a matsayin shugaban taron MDDr karo na 77.

A jawabin da ya gabatar, Abdulla Shahid ya jaddada muhimmancin kiyaye imanin da ake da shi. Ya ce, a yayin da ake ta fama da annobar Covid-19, da rikice-rikice, da matsalolin yunwa da talauci da ma sauyin yanayi, kuma tamkar matsaloli na kara ta’azzara, sai dai ainihin matsalar da za mu fuskanta ita ce ta rasa fatan da muke da shi. Kiyaye fatan da muke da shi ba ya nufin mu kawar da kai daga matsalolin da muke fuskanta, a maimakon haka, ya dace a gano karfin da mu ’yan Adam ke da shi, da ma inda za mu dosa in mun hada kanmu.

A gun taron, babban sakataren MDD António Guterres ya gabatar da jawabi yana mai cewa, tsarin cudanyar kasa da kasa na fuskantar kalubalen da ba a taba ganin irinsa ba, a yayin babban taron MDD karo mai zuwa, sai dai tsarin cudanyar kasa da kasa, shi ne fata daya kacal ga dukkanin ’yan Adam. Daga nan sai ya yi kira ga kasa da kasa, da su kama hanyar diplomasiyya, da yin shawarwari, da kuma nuna hakuri da juna.  (Lubabatu)