logo

HAUSA

Biden ya alkawarta yin taka tsantsan game da ta'addanci

2022-09-12 16:07:12 CMG Hausa

Shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya halarci bikin cika shekaru 21 da kai harin ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2001 da ma'aikatar tsaron kasar ta Pentagon ta shirya jiya Lahadi.

Biden ya bayyana cewa, yana fatan za a tuna cewa, a tsakiyar wadannan kwanaki na bakin ciki, an yi tunani mai zurfi. Ya ce, an kula da juna. Kuma an hallara tare.

Ya kara da cewa, ba za a sarara ba, ba za a taba mantawa ba, ba za a yi kasa a gwiwa ba,inda ya lashi takwabin ci gaba da yaki da ta'addanci.

Shugaban kasar da sauran wadanda suka halarci bikin, sun yi nuni da cewa, barazanar ta'addanci ta yadu a fadin duniya cikin shekaru 21 da suka gabata, kuma akwai hanyoyi mafiya dacewa, wajen yakar ta fiye da aika sojoji da yaki ba tare da izini ba.

Biden kuma ya tabbatar da cewa: "Alkawarinmu na dakile sake kai hari kan Amurka yana nan daram."

A ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2001 ne, wasu maharan suka kwace iko da jiragen sama na kasuwanci guda hudu, daga nan kuma suka kutsa kan cibiyar kasuwanci ta duniya dake birnin New York, da Pentagon da kuma filin Pennsylvania, inda suka halaka kusan mutane dubu 3. (Ibrahim)