logo

HAUSA

Mataimakin shugaban kasar Sin ya sanya hannu kan littafin ta'aziyyar sarauniyar Ingila

2022-09-12 20:32:15 CMG Hausa

Yau ne, mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan, ya ziyarci ofishin jakadancin Burtaniya dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda ya sanya hannu kan littafin ta'aziyyar sarauniya Elizabeth ta biyu, wadda ta rasu tana da shekaru 96 a duniya.

Yayin ziyarar tasa, Wang ya yi shiru na wani dan lokaci a gaban hoton marigayiya sarauniyar Burtaniya, kafin ya sanya hannu a littafin.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, a madadin shugaba Xi Jinping da gwamnatin kasar Sin da jama'ar kasar Sin baki daya, Wang ya nuna jimami tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalan gidan sarautar Burtaniya, gwamnati da al’ummar kasar. (Ibrahim)