logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 6.8 da ta afku a lardin Sichuan ya kai 93

2022-09-12 16:02:40 CMG Hausa

Mahukunta a lardin Sichuan na kasar Sin sun sanar a ranar Litinin da ta gabata cewa, mutane 93 sun mutu, yayin da wasu 25 suka bace, bayan da wata girgizar kasa mai karfin maki 6.8 da ta afku ranar 5 ga watan Satumba, a gundumar Luding da yankunan dake makwafta da ita, da ke kudu maso yammacin lardin Sichuan na kasar Sin.

A cewar hedkwatar ceto, mutane 55 daga cikin wadanda suka mutu, ya faru ne a yankin Ganzi mai cin gashin kansa na jihar Tibet, inda Luding yake, yayin da aka bayar da rahoton mutuwar mutane 38 a birnin Ya'an da karfe 5 na yammancin jiya.

Daga cikin mutanen da suka bace, 9 sun kasance a Luding, sai 16 a Ya’an dake gundumar Shimian.(Ibrahim)