logo

HAUSA

Guterres: Ya dace a kara karfafa hada kai yayin gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa

2022-09-12 15:37:15 CMG Hausa

Yau 12 ga watan Satumba, rana ce ta hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa ta MDD, inda babban sakataren majalisar Antonio Guterres ya bayyana a cikin jawabin da ya gabatar cewa, muddin aka kara karfafa hada kai tsakanin kasashe masu tasowa, hakika za a iya dakile kalubale da tashe-tashen hankula da ba a taba ganin irinsu a tarihi ba, tare kuma da cimma nasarar hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa.

Guterres ya kara da cewa, hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa da hadin gwiwa tsakanin bangarori uku suna da muhimmiyar ma’ana ga kasashe masu tasowa yayin da suke fuskantar sauyin yanayi da matsalolin kiwon lafiya da kuma tabbatar da muradun dauwamammen ci gaba a fannoni 17.

Guterres ya jaddada cewa, dabarun raya kasashe masu tasowa suna da muhimmanci matuka, don haka, dole ne a kara habaka amfanin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa da kuma bangarori uku, yayin da ake kokarin dakile kalubalen dake gaban daukacin bil Adama, kuma yana ganin cewa, kamata ya yi dukkanin kasa da kasa su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, ta yadda za a gina kyakkyawar makoma mai adalci ga bil Adama.

Hakazalika, Guterres ya yi tsokaci cewa, ya zama wajibi a kara mai da hankali kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa da hadin gwiwar dake tsakanin bangarori uku, a kokarin da ake na fardado da tattalin arzikin duniya, kuma akwai bukatar kasashe masu tasowa su bayar da gudummawa, domin gina tattalin arziki da zaman takewar al’umma masu juriya da karfi, tare kuma da cimma burin samar da dauwamammen ci gaba yadda ya kamata. (Jamila)