logo

HAUSA

An Mika Cibiyar Wasannin Motsa jiki Da Al'adu Da Kasar Sin Ta Samarwa Tunisia

2022-09-11 16:51:35 CMG Hausa

Rahotanni daga kasar Tunisia na cewa, an yi nasarar damka cibiyar wasanni da al'adun matasa ta Ben Arous da kasar Sin ta ba da taimako wajen samar da ita, a arewa maso gabashin Tunisiya.

Jami’i mai kula da aikin gina cibiyar dake aiki a ma’aikatar kula da kayayyakin aikin kasar Nizar Zoghlami ne ya bayyana hakan a ranar Juma'ar da ta gabata, a wani bikin mika cibiyar da ya gudana a lardin Ben Arous. Yana mai cewa, nan ba da jimawa ba, za a bude cibiyar ga jama'a wadda ake fatan za ta kuma kawo farin ciki ga 'yan kasar Tunisiya.

Ya bayyana cewa, ma'aikatan kasar Sin sun shawo kan wahalhalu da suka kunno kai ba zato ba tsammani yayin aikin gina cibiyar, musamman a sakamakon tasirin annobar COVID-19.

Darektar sashen samar da ababen more rayuwa na ma'aikatar matasa da wasanni ta kasar Tunisia, Naoufel Bel Haj Rhouma, ta mika godiyar ma'aikatarsa ga bangaren kasar Sin.

Rhouma ta ce, ma'aikatan gine-gine na kasar Sin, suna da aminci kuma sun kammala shirin a kan lokaci.(Ibrahim)