Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta mika wa Amurka kokenta kan kutsen intanet da ta yiwa jami'ar kasar Sin
2022-09-11 20:10:14 CMG Hausa
A cewar shafin intanet na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, a ranar 8 ga Satumban shekarar 2022 da muke ciki ne, babban darektan sashen kula da harkokin Amurka da Oceania na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Yang Tao, ya gabatarwa ofishin jakadancin Amurka dake kasar Sin koke, game da kutsen da Amurkar ta yiwa kwanfutocin jami'ar Northwestern Polytechnic ta kasar Sin.(Ibrahim)