logo

HAUSA

Guturres: Kasashe masu sukuni ne ke da alhakin mafi yawa na fitar da hayakin dake gurbata muhalli

2022-09-11 16:47:57 CMG Hausa

Magatakardan MDD, Antinio Guterres ya bayyana cewa, kasashe masu karfin tattalin arziki ne ke da alhakin mafi yawa, na fitar da gurbacewar iskar gas dake gurbata yanayin duniyarmu a tsawon tarihi.

Babban sakataren ya bayyana haka ne, a wata ganawa da manema labarai a birnin Karachi dake kudancin Pakistan jiya Asabar, a yayin ziyarar da ya kai yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a kasar.

Ya kara da cewa, wadannan tasiri da muke fuskanta suna dada karuwa, kuma mutanen da ke rayuwa a cikin matsanancin yanayi ciki har da kudancin Asiya, sun fi fuskantar barazanar yiwuwar mutuwa sau 15 sakamakon tasirin matsalar sauyin yanayi.

Guterres ya ce, kusan rabin bil-adama yanzu haka, suna cikin wannan rukuni, kuma da dama daga cikinsu, suna zaune ne a kasashe masu tasowa

Sakamakon bala'in ambaliyar ruwan da kasar Pakistan ke fama da shi, babban sakataren ya yi kira ga kasashen duniya, da su bullo da wani sabon salon yafe basussuka ga kasashen da abin ya shafa.

Ya kuma kara bayar da shawarar tsari na yin musanya basussuka da ya kamata wata kasa, maimakon biyan basussukan da masu lamuni ke bin ta, sai ta yi amfani da wannan kudi, wajen saka hannun jari a bangaren jurewa matsalar sauyin yanayi, da samar da ababen more rayuwar jama’a mai dorewa da kuma sauya tsarin tattalin arzikinsu wanda ba ya gurbata muhalli. (Ibrahim)