logo

HAUSA

An Tattauna Kan Wasu Daftarorin Da Za A Yi Nazarinsu Yayin Zaman Kwamitin Kolin JKS

2022-09-10 20:03:45 CMG Hausa

Ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya gudanar da taro domin tattaunawa kan daftarorin da za a gabatar domin nazarinsu yayin zama na 7 na kwamitin kolin JKS na 19.

Taron na jiya, wanda Xi Jinping, sakatare janar na kwamitin kolin JKS ya jagoranta, ya tattauna kan daftarin rahoto na kwamitin kolin na 19 da za a mika ga babban taron wakilan JKS karo na 20, da daftarin yi wa kundin tsarin JKS garambawul da daftarin rahoton aiki na hukumar kolin JKS mai sa ido kan da’a, wanda za a mika ga babban taron wakilan JKS karo na 20.

Har ila yau, ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin na 19, ya tattauna kan rahoton aiwatar da wasu matakai 8 na inganta jam’iyyar da ayyukan gwamnati, da kuma rahoton aiki na gano wasu dabaru marasa amfani da rage matsi kan kananan hukumomi, tun bayan babban taron wakilan JKS karo na 19. (Fa’iza Mustapha)