logo

HAUSA

Kasar Sin Muhimmiyar Abokiyar Hulda Ce Da Afrika Za Ta Iya Hada Hannu Da Ita Wajen Yaki Da Yunwa

2022-09-10 16:02:59 CMG Hausa

Wani masanin tattalin arziki na kasar Rwanda Egide Karuranga, ya bayyana kasar Sin a matsayin daya daga cikin muhimman kasashen duniya da kasashen Afrika za ta iya hada hannu da su, wajen yaki da karancin abinci a nahiyar, saboda gogewar da take da shi da tarin fasahohin aikin gona.

Masanin na kasar Rwanda ya bayyana haka ne jiya, yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, a gefen taron raya muhalli na Africa Green Revolution da aka kammala a Kigali, babban birnin kasar.

A cewarsa, Afrika na iya koyon dabarun kasar Sin bisa la’akari da yadda Sin din ta yi nasarar yaki da yunwa da tamowa.

Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta iya zuba jari a bangaren samar da ruwa da noman rani, yana mai bayyana su a matsayin tubalin dake bukatar mayar da hankali kansu fiye da komai a tsarin matakan raya tattalin arziki.

Ya ce misali, Afrika na gwagwarmaya da noman rani da samun amfanin gona, amma Sin tana da matukar gogewa a wannan fanni. Haka kuma, akwai kirkire-kirkiren fasahohin aikin gona da tuni aka gwada, aka aiwatar tare da ganin nasararsu a kasar Sin, wadanda za a iya amfani da su a nahiyar Afrika. (Fa’iza Mustapha)