logo

HAUSA

CMG ta watsa shagalin murnar bikin tsakar yanayin kaka ta shekarar 2022

2022-09-10 20:34:26 CMG Hausa

Bikin tsakar yanayin kaka yana daya daga cikin manyan bakukuwan gargajiya na kasar Sin. A wannan rana, Sinawa su kan hadu, tare da kallon duniyar wata, da cin wainar wata, da tunawa da sauran ‘yan uwa tare da yi wa juna fatan alheri. A daren ranar 10 ga watan Satumba, wato ranar bikin tsakar yanayin kaka bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ya watsa shagalin murnar bikin na shekarar 2022, inda aka nuna shirye-shirye masu nishadantarwa ga masu kallo na sassan duniya.

Taken shagalin murnar bikin tsakar yanayin kaka na bana shi ne, al’adun duniyar wata, inda shagalin ya nuna al’adun bikin tsakar yanayin kaka da tunanin gida da kuma haduwar iyalai ta hanyoyin shirye-shiryen kide-kide da wake-wake da raye-raye. Ta hakan, masu kallo za su iya gano al’adun bikin da kaunar da Sinawa ke yi masa.

A bana, kafofin watsa labaru na kasashen waje da dama ciki har da na Amurka, da Canada, da kasashen Turai, da Japan, da Kenya da sauransu, sun watsa shirye-shiryen shagalin da CMG ya gabatar.

A bikin na bana, ‘yan saman jannati dake kumbon Shenzhou-14 Chen Dong, da Liu Yang, da Cai Xuzhe sun yi murnar bikin, wanda shi ne karo na farko da Sinawa suka yi murnar bikin a sararin samaniya. ‘Yan saman jannati uku sun dauki bidiyo don yi wa dukkan Sinawa a sassan duniya fatan alheri. (Zainab Zhang)