logo

HAUSA

Wang Yi ya taya James Cleverly murnar zama sabon ministan harkokin wajen Birtaniya

2022-09-10 16:51:05 CMG Hausa

Memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya mika sako ga James Cleverly, don taya shi murnar zama sabon ministan harkokin wajen kasar Birtaniya.

A cikin sakon, Wang Yi ya bayyana cewa, Sin da Birtaniya kasashe ne membobin kwamitin sulhu na MDD na dindindin, wandanda suke kawo wa duniya babban tasiri a fannoni daban daban. Haka kuma ya ce yana fatan bangarorin biyu za su bi ka’idojin girmama juna da samun moriyar juna, da kara hadin gwiwa da mu’amala, da daidaita matsalolin dake akwai a tsakaninsu, don sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata. (Zainab)