logo

HAUSA

Masana Kimiyyar Kasar Sin Sun Gano Wani Sabon Ma’adini Da Aka Dauko Daga Duniyar Wata

2022-09-09 19:56:49 CMG Hausa

Masana kimiyya na kasar Sin, sun gano wani sabon ma’adini da aka sanyawa suna Chang'esite-(Y), wanda kumbon Chang'e-5 ya kwaso daga duniyar wata.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa, da hukumar lura da ayyukan binciken samaniya ta kasar ko CNSA, da hukumar lura da makamashin Atomic ta kasar ko CAEA suka fitar a Juma’ar nan, an ce an tantance sabon ma’adinin ne bayan zurfafa binciken kimiyya.

Da yake karin haske kan hakan, mataimakin daraktan hukumar ta CAEA Dong Baotong, ya ce wannan ne karon farko a tarihi da kasar Sin ta gano wani ma’adini a duniyar wata, kuma karo na 6 da dan Adam ya cimma nasarar yin hakan. Da wannan sakamako kuma, kasar Sin ta zamo kasa ta 3 a duniya, da ta taba yin nasarar gano sabon ma’adini a doron duniyar wata.

Ma’adinin Changesite-(Y), dutse ne mai yanayi irin na kankara. Kuma tuni sashen tantance sabbin ma’adinai da sanya musu sunaye, dake karkashin babbar hukumar masana albarkatun ma’adinai ta duniya, ta amince da sabon ma’adinin a hukumance.  (Saminu Alhassan)