logo

HAUSA

MDD ta yi kira da a dakatar da tashin hankali a Sudan ta Kudu

2022-09-09 10:18:38 CMG Hausa

Babbar jami'ar kula da ayyukan jin kai ta MDD dake Sudan ta Kudu Sara Beysolow Nyanti, ta yi kira da a gaggauta dakatar da kai hare-hare, biyo bayan sake barkewar rikici a jihar Upper Nile, wanda ya raba dubban mutane da muhallansu.

Jami’ar, ta yi Allah wadai da kazamin fadan da aka gwabza, tsakanin bangarorin da ke dauke da makamai a garin Tonga da yankunan dake makwafta da gundumar Panyikang a jihar Upper Nile, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula, da jikkata wasu da kara tilasta mutane barin muhallansu.

Nyanti ta ce, rahotannin da ba a tabbatar da su ba na cewa, an kashe mutane kusan 300 a hare-haren. Tana mai cewa, masu aikin jin kai sun tattara albarkatun da ake da su, kuma suna aiki don samar da taimakon ceton rai don biyan bukatun gaggawa.(Ibrahim)