logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya gabatar da sakon ta’azziya ga sabon sarkin Ingila game da rasuwar sarauniya Elizabeth II

2022-09-09 14:11:31 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da sakon jaje ga sabon sarkin Ingila, Charles Philip Arthur George Mountbatten-Windsor, game da rasuwar sarauniyar Ingila, Elizabeth II, inda a madadin gwamnati da jama’ar kasar Sin, Xi ya nuna matukar alhinin rasuwarta, da jajantawa masarauta, da gwamnati gami jama’ar Birtaniya baki daya.

A yau Jumma’a kuma, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya aike da sakon ta’azziya zuwa ga takwararsa ta Birtaniya, Liz Truss, game da rasuwar sarauniya Elizabeth II. (Murtala Zhang)