logo

HAUSA

Jakadan Sin a Nijar ya gana da minstan harkokin wajen Nijar

2022-09-09 11:31:21 CMG HAUSA

 

Jakadan kasar Sin dake jamhuriyar Nijar Jiang Feng, jiya Alhamis ya gana da karamin ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasar Nijar Hassoumi Massoudou, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayoyi kan dangantakar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu.

Jiang ya bayyana cewa, kasar Sin na dora muhimmanci matuka kan raya dangantakar dake tsakaninta da jamhuriyar Nijar, kuma tana son ci gaba da zurfafa hadin gwiwa a aikace tare da ita, a fannoni daban daban, bisa tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC), da kokarin raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka da kuma al’ummomin Sin da jamhuriyar Nijar mai makomar bai daya a sabon zamani.

Hassoumi Massoudou ya yi bayani mai zurfi game da kyakkyawan ci gaban da aka samu, wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, tare gode wa kasar Sin bisa taimakon da take bayarwa ga ci gaban Nijar a fannoni daban daban. Ya kuma bayyana cewa, Jamhuriyar Nijar na son yin aiki da kasar Sin, don samun sabbin ci gaba a hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannoni daban-daban don moriyar kasashen biyu da al'ummominsu. (Ibrahim Yaya)