logo

HAUSA

Sin Ta Taya Shugaban Angola Murnar Sake Lashe Babban Zabe

2022-09-09 19:22:06 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce Sin ta yi maraba da nasarar gudanar da babban zabe a kasar Angola, tare da taya shugaban kasar mai ci João Lourenço murnar lashe zaben da ya gudana.

Mao Ning, wadda ta bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa na yau Juma’a, ta ce Sin da Angola sun zurfafa kawancen su daga dukkanin fannoni, sun kuma ci gaba da gudanar da ingantaccen hadin gwiwa a shekarun baya-bayan nan. Kaza lika Sin na dora matukar muhimmanci ga bunkasar alakar ta da Angola, kuma a shirye take ta yi aiki tare da Angola, wajen ingiza sabbin nasarori, karkashin hadin gwiwar kawancen dake tsakanin kasashen biyu.

A jiya Alhamis ne kotun kundin tsarin mulkin Angola, ta yi watsi da karar da tsagin ‘yan adawar Angolar suka gabatar, suna masu kalubalantar sakamakon zaben da ya baiwa shugaban kasar mai ci nasara.

Bisa sakamakon da hukumar zaben kasar mai zaman kan ta ta fitar, jam’iyyar MPLA mai mulkin kasar, ta samu kashi 51.17 bisa dari, na daukacin kuri’un da aka kada, wanda hakan ya baiwa shugaba Lourenço nasarar yin tazarce a kujerar shugabancin kasar.   (Saminu Alhassan)