logo

HAUSA

Sin da Afirka na da imani game da raya makoma ta bai daya tsakaninsu

2022-09-09 19:32:23 CMG Hausa

Yau Jumma’a ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da shugaban karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka AU, kana shugaban kasar Senegal Macky Sall, suka aike wa juna sakon murnar cika shekaru 20 da kafa kungiyar AU, da kulla alakar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da AU.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yau cewa, wannan ne karo na farko a tarihin raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, wanda ya shaida imanin da suka yi da juna a fannonin sada zumunta, da hadin gwiwa, da neman raya makoma ta bai daya tsakaninsu.

Mao Ning ta jaddada cewa, Sin ta dora muhimmanci sosai kan raya dangantakar dake tsakaninta da kungiyar AU, da maida kungiyar AU a matsayin muhimmiyar abokiya ta hadin gwiwa, yayin da ake yin kokarin raya hadin gwiwa da sada zumunta a tsakanin Sin da Afirka, har ma da sauran kasashe masu tasowa, da kuma nuna goyon baya ga kungiyar AU wajen taka muhimmiyar rawa kan harkokin Afirka da kasa da kasa.

Ta ce Sin tana son yin kokari tare da kungiyar AU, wajen kara yin mu’amala da juna, da imani da juna kan harkokin siyasa, da fadada hadin gwiwa, da nuna goyon baya ga juna, kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu, ta yadda hakan zai sa kaimi ga daga dangantakar dake tsakanin Sin da kungiyar AU, da Afirka zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)