logo

HAUSA

Yarima Charles ya zama sarkin Burtaniya

2022-09-09 09:39:40 CMG HAUSA

 

Fadar Buckinghan ta sanar da Charles Philip Arthur George Mountbatten-Windsor, babban dan sarauniya Elizabeth ta II, a matsayin sabon sarkin Ingila, bayan rasuwar sarauniya Elizabeth ta biyu

Sarauniya Elizabeth ta biyu, wadda ita ce basarakiya mafi dadewa a kan gadon sarauta a Britaniya a tarihi, ta rasu jiya tana da shekaru 96.

A safiyar yau ne, fadar Buckingham ta sanar da cewa, basarakiyar tana karkashin kulawar likitoci, saboda damuwar likitoci game da lafiyarta. Kuma ba da dadewa ba, 'yan gidan sarautar suka garzaya zuwa Scotland don kasancewa tare da ita bayan fitar da sanarwar.

A matsayin wani bangare na tsarin mulkin Biritaniya, an mika rawanin sarautar ga babban danta Charles Philip. Sai dai ba a san lokacin da za a gudanar da bikin nadin sarautar a hukumance ba.

Magadakardan MDD Antonio Guterres ya fada jiya Alhamis cewa, ya yi alhinin rasuwar sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu. Guterres ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, "Na yi matukar bakin ciki da rasuwar mai martaba sarauniya Elizabeth ta biyu, sarauniyar Ingila da arewacin Ireland,".

Ya kuma mika ta'aziyyarsa ga iyalan sarauniyar, gwamnati da al'ummar Biritaniya, da sauran kasashe renon Ingila wato Commonwealth. (Ibrahim Yaya)