logo

HAUSA

Gwamnatin HKSAR na maraba da sanya yankin a matsayin mafi ’yancin tattalin arziki a duniya

2022-09-09 10:21:38 CMG HAUSA

 

Gwamnatin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin (HKSAR), ta yi maraba da yadda cibiyar Fraser ta kasar Canada, ta sake bayyana yankin a matsayin mafi 'yancin tattalin arziki a duniya a rahoton shekara ta 2022 dake bayyana kasashe da yankuna mafiya 'yancin tattalin arziki a duniya.

Yankin na Hong Kong ya zama na farko tun lokacin da aka fara fitar da wannan rahoton.

Mai magana da yawun gwamnatin yankin ya bayyana cewa, hangen nesa, da yadda yankin Hong Kong, ke tafiyar da harkokinsa karkashin tsarin "kasa daya, amma tsarin mulki iri biyu", zai kara taimaka masa wajen samun karfin goyon baya da alaka da babban yanki da kasuwannin duniya, da ci gaba da taka rawar musamman da ya saba, da samar da karfi na ci gaba, da shiga a dama da shi a harkokin cikin ci gaban kasar baki daya.  

Kakakin ya kara da cewa, yankin musamman na Hong Kong, zai ci gaba da yin amfani da dabarun kasa, kamar shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14, da raya yankin musamman na Guangdong-Hong Kong-Macao da ake kira Greater Bay, da hadin gwiwar raya shawarar ziri daya da hanya daya mai inganci, tare da yin amfani da damar da ke tafe. (Ibrahim Yaya)