logo

HAUSA

An cimma sakamako guda 1339 yayin taron CIFTIS

2022-09-08 20:06:44 CMG Hausa

A yau taron manema labarai da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta saba shiryawa a yau Alhamis, kakakin ma’aikatar Shu Jueting ta bayyana cewa, alkaluman kididdigar farko sun nuna cewa, an cimma sakamako guda 1339 yayin taron baje kolin cinikayyar hidima na kasa da kasa na kasar Sin CIFTIS na shekarar 2022. Kuma, an gabatar da wasu muhimman rahotanni, ciki har da rahoton “Bunkasuwar cinikayyar hidima ta kasar Sin”, gami da sakamakon da aka cimma.

A yayin taro na wannan karo, an shirya dandalin tattaunawa na koli guda 7, da tarukan karawa juna sani sama da 100, inda aka mai da hankali kan sana’o’i masu ci gaba da kuma yin musayar ra’ayoyi kan sabbin fasahohi, domin ba da gudummawa kan yadda za a raya tattalin arziki da cinikayyar kasashen duniya. Haka kuma, an nuna yadda cinikayyar hidima ta bunkasa a kasar Sin, inda aka kulla wasu muhimman yarjejeniyoyin hadin gwiwa tsakanin sassa daban daban. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)