logo

HAUSA

Kamfanin Sin ya kammala aikin gina tashar samar da lantarki ta Ruzibazi a Burundi

2022-09-08 13:45:28 CMG Hausa

An yi bikin murnar kammala aikin gina tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa ta Ruzibazi da kamfanin kasar Sin ya yi a kasar Burundi a ranar 6 ga wata. Shugaban kasar Evariste Ndayishimiye ya halarci bikin, tare gabatar da jawabi, inda ya yabawa namijin kokarin da kamfanin kasar Sin ya yi wajen kammala aikin a kan lokaci.

Shugaba Ndayishimiye ya nuna jin dadinsa ga bangaren kasar Sin, bisa hadin gwiwar da take yi da kasar Burundi a fannonin samar da ababen more rayuwa da aikin gona, ya kuma yaba wa kasar Sin kan yadda ta shawo kan matsaloli da dama da annobar ta haifar, da kuma kammala aikin kamar yadda aka tsara.

A nata bangaren, jakadar kasar Sin dake Burundi Zhao Jiangping ta bayyana cikin jawabin da ta gabatar yayin bikin cewa, kammala aikin gina tashar Ruzibazi, zai kasance sabon mafari na hadin gwiwa tsakanin Sin da Burundi bisa jagorancin "Ayyuka tara" na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. Ta kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da tallafawa Burundi da sauran kasashen Afirka, wajen raya makamashi da ake iya sabuntawa don samun wadatar makamashi. An fara aikin gina tashar samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da karfin ruwa ta Ruzibazi ne tun daga watan Oktoban shekarar 2018, kuma an kammala aikin gwajin na’urar ta karshe, daga baya na’urori uku sun fara aiki a watan Yulin bana. (Jamila)