logo

HAUSA

Dandalin BRICS ya himmatu wajen inganta ci gaban mai dorewa tare

2022-09-08 14:06:49 CMG Hausa

Jiya ne, aka bude taron dandalin tattaunawa na kasashen BRICS, taron da ke mayar da hankali kan zurfafa hadin gwiwa, don inganta masana'antu, da kokarin samun ci gaba mai dorewa tare, a birnin Xiamen na lardin Fujian dake yankin gabashin kasar Sin.

BRICS wato kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa, sun hada da Brazil, da Rasha, da Indiya, da Sin da Afirka ta Kudu.

Mutane fiye da 300, da suka hada da wakilan diflomasiyya da kungiyoyin kasa da kasa, da kamfanoni da kungiyoyin masana'antu ne, suka halarci taron ta yarar gizo ko kuma kai tsaye.

An kuma gudanar da tattaunawa mai zurfi kan zamanintar da hadin gwiwar masana'antu da tsarin samar da kayayyaki da ci gaban masana’antu mai dorewa da sauransu. (Safiyah Ma)