logo

HAUSA

Xi Jinping ya karfawa daliban jami’a gwiwar koyon ilmin malanta don taimakawa yankuna masu karancin ci gaba

2022-09-08 15:24:09 CMG HAUSA

 

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da daliban jami’ar horar da malamai ta Beijing suka rubuta masa a jiya Laraba, daliban da suke koyon ilmin malanta don tallafawa yankuna masu karancin ci gaba dake yankin tsakiya da yammacin kasar.

Shugaba Xi ya yi musu kyakkyawar fata yayin da ake bikin cika shekaru 120 da kafuwar jami’ar da ranar malamai karo na 38, inda shugaba Xi ya yiwa dukkanin malamai a kasar fatan alheri.

A cikin wasikar da ya rubutawa wadannan dalibai, shugaba Xi ya ce, tun lokacin da kuka shiga makarantar shekara guda, kun kara iliminku, da fadada hangen nesa, da karfafa imaninku kan koyarwa da ilimantar da jama'a daga tushe ta hanyar nazarin azuzuwa da aikin koyarwa na sa kai, ina murna sosai. Ban da wannan kuma, Xi Jinping ya ce, ina fatan za ku kara kaimi wajen fadakar da jama’a, koyarwa, da warware dambarwa, bayan kammala karatunku, kana za ku shiga inda jama'a suka fi bukata, da kokarin zama malami na-gari. (Amina Xu)