logo

HAUSA

Xi Ya Yi Kira Da A Kara Azama Kan Masana'antu Wajen Yin Kirkire-kirkire

2022-09-08 19:33:42 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a kara azama kan kamfanoni da su yi kirkire-kirkire, da samar da karin kanana da matsakaitan masana'antu, wadanda suka kware da kuma kirkire-kirkire.

Xi, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kwamitin koli na soja, ya bayyana haka ne a cikin wata wasikar taya murna da ya aikawa wani taro game da ci gaban wadannan kamfanoni, wanda aka bude Alhamis din nan a birnin Nanjing na lardin Jiangsu dake yankin gabashin kasar Sin.(Ibrahim)