logo

HAUSA

Guterres ya kira da a yi kokarin magance gurbatar iska

2022-09-08 13:41:00 CMG Hausa

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya gabatar da wani jawabi ta kafar bidiyo jiya Laraba dake zama ranar iska mai tsabta ta kasa da kasa karo na uku, inda ya yi kirayi ga kasashen duniya, da su hada kai don magance gurbatar iska.

Guterres ya ce, iska mai tsabta, da yanayi mai kyau, da muhallin hallitu mai inganci, su ne hakkin bil Adama, amma yanzu kaso 99 cikin 100 na al’ummomi a fadin duniya, suna da gurbacewar iska, lamarin dake haifar da dumamar doron duniyarmu, da haddasa karuwar gobarar daji.

Don haka, ya yi kira a kara zuba jari a bangaren makamashin da ake iya sabuntawa, kuma a rage fitar da iskar carbon, a sa’i daya kuma, a ci gaba da sa ido kan gurbacewar iska, da tsara dokoki da manufofin da abin ya shafa.

Ya kuma jaddada cewa, ana sa ran matakan da aka dauka, za su ceci miliyoyin rayuka a fadin duniya a ko wace shekara, kuma za su dakile matsalar sauyin yanayi, tare kuma da hanzartar dauwamammen ci gaba. (Jamila)