logo

HAUSA

Takunkumi na kashin kai da wasu kasashe suka sanya ya kawo illa ga tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa

2022-09-08 20:15:41 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru Alhamis din nan cewa, wasu kasashe sun yi watsi da tsarin mulkin MDD da ka’idojin dokokin kasa da kasa, tare da sanya takunkumi ba bisa ka'ida ba kan wasu kasashen da suka ga dama, lamarin da ya yi matukar tasiri ga tsarin siyasa da tattalin arziki na duniya da tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa.

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana a gun taron tattaunawa kan tattalin arzikin yankin gabashin kasar Rasha a kwanakin baya cewa, takunkuman da kasashen yammacin duniya suka kakabawa kasarsa, sun kasance barazana mafi tsanani a duniya, wanda ya maye gurbin annobar cutar COVID-19. Kasar Amurka ta lalata tsarin tattalin arzikin duniya da aka kafa har na tsawon shekaru fiye da 100, da tsara ka’idojin da ke da amfani a gare ta da bisa manufar da ta tsara, a yunkurin hana ci gaban tarihi.

Game da batun ziyarar da wasu ‘yan majalisar dokokin kasar Amurka suka kai a yankin Taiwan na kasar Sin, Mao Ning ta jadadda cewa, Sin ta kalubalanci jami’an kasar Amurka da abin ya shafa, da su bi ka’idar Sin daya tak a duniya, da ka’idojin hadaddiyar sanarwar hadin gwiwa guda uku da Sin da Amurka suka cimma, da dakatar da duk wani nau’in mu’amala a hukumance da yankin Taiwan, da dakatar da nuna goyon baya ga ‘yan aware na yankin Taiwan. (Zainab)