logo

HAUSA

Mutanen da suka mutu sanadiyyar girgizar kasa a Luding sun karu zuwa 82

2022-09-08 15:09:31 CMG Hausa

Rahotannin da sashen ba da ceton gaggawa kan girgizar kasa da ta auku a gundumar Luding ta lardin Sichuan na kasar Sin a ranar 5 ga wannan wata ya gabatar sun nuna cewa, ya zuwa safiyar yau Alhamis da misalin karfe 8, adadin mutanen da suka rasu sanadiyyar girgizar kasa mai karfin maki 6.8, ya karu zuwa 82, daga ciki, mazauna gundumar Luding ta yankin Ganzi da suka mutu sun kai 46, sai 36 daga gundumar Shimian ta birnin Ya’an, yayin da wasu 35 sun bace, kana mutane sama da 270 sun ji rauni. (Jamila)