logo

HAUSA

Truss ta zama firayin ministar Birtaniya

2022-09-07 10:22:30 CMG Hausa

An rantsar da shugabar jam’iyyar masu ra’ayin rikau wato conservative dake rike da mulki a kasar Birtaniya Elizabeth Truss, a matsayin firayin ministar kasar a hukumance jiya Talata a birnin Landan, fadar mulkin kasar, inda ta kasance firayin minista mace ta uku a tarihin kasar ta Birtaniya bayan Margaret Thatcher da Theresa May.

Kamar yadda aka saba, firayin minista Boris Johnson, ya gabatar da takardarsa ta yin murabus ga sarauniyar kasar Elizabeth II a Scotland jiya, kuma ta amince. Daga baya Truss ta samun amincewar sarauniya don kafa sabuwar majalisar ministoci, domin fara mulki a kasar a hukumance.

Truss ta gabatar da wani jawabi bayan da ta dawo fadar firayin minista mai lamba 10 dake kan titin Downing a birnin Landan, inda ta bayyana cewa, za ta mai da hankali kan ayyukan daidaita matsalolin da kasar ke fuskanta a bangarorin ci gaban tattalin arziki da rikicin makamashi da kiwon lafiya da sauransu, bayan da ta fara aiki kan mukaminta na firayin minisnta kasar. (Jamila)