logo

HAUSA

Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Zababben Shugaban Kenya

2022-09-07 19:12:39 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga zababben shugaban kasar Kenya William Ruto a yau Laraba.

Cikin sakon, shugaba Xi ya ce, Sin da Keyan na da daddadiyyar alakar abota da hadin gwiwa a bangarori da dama, wadanda suka haifar da kyawawan sakamako a shekarun baya-bayan nan.

Ya ce yana ba ci gaban huldarsu muhimmanci, kuma a shirye yake ya hada hannu da shugaba Ruto, wajen daukaka huldar zuwa wani muhimmin matsayi domin moriyar kasashen biyu da al’ummominsu. (Fa’iza Mustapha)