logo

HAUSA

Sin ta yi imani da cimma nasarar yaki da ibtila’i

2022-09-07 20:43:55 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, bayan abkuwar girgizar kasa a gundumar Luding ta lardin Sichuan a ranar 5 ga wannan wata, kasashe da dama ciki har da kasar Rasha, sun jajantawa kasar Sin ta hanyoyi daban daban, kana suna son nuna goyon bayansu ga Sin ta hanyar bayar da da gudummawar yaki da ibtila’in.

Da take bayyana godiyar kasar Sin gare su, Mao Ning ta jaddada cewa, gwamnatin kasar tana kokarin gudanar da ayyukan yaki da ibtila’in da ayyukan ceto, kuma masu aikin ceto sun isa yankin da lamarin ya auku, domin neman mutanen da suka bace, da jinyar wadanda suka ji raunuka, da tsugunar da wadanda lamarin ya rutsa da gidajensu, da daidaita sauran harkokin yau da kullum a yankin.

Bugu da kari, ta ce Sin ta yi imanin za ta yaki ibtila’in, da farfado da zaman rayuwar jama’ar yankin. (Zainab)